Shugaban Sudan ya kaddamar da shirin zaman lafiya a Darfur

Shugaba Omar Al -Bashir na Sudan

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana shirin kaddamar da hukumar kula da yankin Darfur

Shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir ya kaddamar da Hukumar mulki ta Yankin Darfur.

Hukumar za ta rika kula da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar yankin Darfur mai fama da rikice rikice tun shekarar 2003.

Yarjejeniyar zaman lafiyar wadda aka rattabawa hannu a Doha a bara, ta bayar da daman raba madafun iko da arzikin kasa.

Yarjejeniyar ta kuma yi tanadin biyan diyya ga wadanda rikicin ya shafa; dawo da wadanda suka rasa matsugunansu;da inganta tsaron lafiyar al'umma.

Kungiya daya ce kadai ta rattaba hannu kan yarjejeniyar, yayin da sauran ukku suka ki amincewa da ita.

Sai dai kuma tuni manyan kungiyoyin 'yan tawayen yankin suka yi watsi da matakain.