Turkiyya za ta kaddamar da wani yunkurin difilomasiyya a kan Syria

Firaministan Turkiyya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firaministan Turkiyya

Gwamnatin kasar Turkiyya na shirin kaddamar da sabon shirin difilomasiyyar da zai yi matsin lamba kan Shugaba Bashar al Assad don ya kawo karshen rikicin kasar Syria.

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya ce gwamnatinsa a shirye take da karbi bakuncin babban taron kasa da kasa da zai haifar da hadin kan mutanen kasar Syria.

Kafin wucewarsa Washington domin tattaunawa, Ahmet Davutoglu ya ce, "Idan har Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ba zai iya kare rayukan fararen hula ba, to ya kamata sauran kasashen da ra'ayoyinsu suka zo daya su samu hanyoyin da za su bi na taimakawa."

Sai da Firaministan kasar Russia, Vladimir Putin ya yi gargadi game da tsoma bakin kasashen waje kan harkokin kasar ta Syria.

Yayin da yake yin misali da kasashen Syria da Libya, Mr Putin, ya ce akwai alamun ruruwar wutar rikicin daga bangaren kasashen wajen.

Karin bayani