Syria na kara kai hare hare a Homs

Hakkin mallakar hoto

Masu fafutuka a gari na ukku mafi girma a Syria, wato Homs, sun ce a yau laraba dinnan an kashe kimanin mutane arba'in a lugudan wutar da dakarun gwamnati ke yi a birnin. Wata kungiyar masu fafutukar ma ta ce akalla jarirai bakwaini goma sha takwas ma sun rasa rayukansu sakamakon dauke wutar lartarki da ta katse aikin na'urar da aka sa su. Wannan dai na zuwa kwana daya bayan ziyarar da ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya kai inda ya gana da shugaba Bashar al Assad kan halin da ake ciki.

A yau dakarun gwamnatin Syrian sun kara tsananta hare-haran da suke kaiwa a garin na Homs. Rahotanni sun ce tankunan yaki da sojoji na kara shiga wasu sassan birnin.

Karin bayani