Rashin daukar mataki kan Syria masifa ce -Ban Ki Moon

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ban Ki Moon

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki Moon, ya ce gazawar kwamatin sulhu na Majalisar wajen daukar mataki game da rikicin da ke faruwa a Syria, tamkar wata masifa ce ta fadawa 'yan kasar.

Mr Ban ya ce matakin zai karawa gwamnatin kasar kaimi wajen ci gaba da cin mutuncin 'ya'yanta.

Ya ce gwamnatin kasar ta kashe dubban 'ya'yanta wadanda ba su da laifi, amma duk da haka shugaban kasar Bashar al- Assad na ikirarin cewa yana kashe-kashen ne da yawun bakin 'yan kasar.

Mr Ban ya yi gargadin cewa luguden wutar da sojin gwamnatin kasar ke yi a birnin Homs na da matukar tayar da hankali, kuma ya nuna cewa gwamnatin shugaba Assad bata da niyyar kawo karshen rikcin da ke faruwa a kasar.

A ranar Asabar ne dai kasashen Rasha da China suka yi watsi da wani kuduri da kungiyar kasashen Larabawa ta gabatar wa kwamatin sulhun, wanda ya nemi yin Alla-wadai da rikicin da ke faruwa a kasar.

Karin bayani