An amince da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati a Girka

Shugabannin siyasar Girka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugabannin siyasar Girka

Ofishin Praministan kasar Girka ya ce, daga karshe dai shugabannin gwamnatin hadin gambizar kasar sun amince da wani sabon shirin tsuke bakin aljihun gwamnati.

A yanzu za a gabatar da yarjajeniyar ga taron ministocin kudi na yankin Euro, a birnin Brussels.

Dole sai da amincewarsu kamin a sake yin belin kasar ta Girka da kudaden da yawansu ya kai Euro biliyan 130.

An dakatar da shirin ne saboda shugabannin siyasar Girkar sun kasa amincewa da batun rage kudaden fansho.

Kungiyoyin kwadago a Girkar sun ce, matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin na kara janyo koma baya ga tattalin arzikin kasar, ganin yadda ake cigaba da fama da rashin aikin yi.

Sun ce nan gaba a cikin wannan makon za su yi yajin aiki na kwana biyu.

Karin bayani