Iran ta samu ci gaban nukiliya -Ahmadinejad

Shugaba Mahmoud Ahmadinejad na Iran Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Mahmoud Ahmadinejad na Iran

Shugaba kasar Iran, Mahmoud Ahmadinejad ya ce nan da 'yan kwanaki kasarsa za ta ba da sanarwa a kan gagarumin ci gaban da kasar ta samu ta fannin nukiliya.

Ya kuma ce masana kimiyyar kasar ta Iran za su taka rawa sosai a wannan al’amari:

"A yau mun ga cewa kasarIranta zama mai karfin nukiliya, kana za ta iya biyan muhimman bukatunta.

"Godiya kuma ta tabbata ga Allah cewa masana kimiyyar Iran za su iya biyan bukatun kasar na nan gaba."