Najeriya na fuskantar rugujewa, in ji shugaban cocin Ingila

Shugaban cocin Ingila Dr. Rowan Williams Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban cocin Ingila Dr. Rowan Williams ya ce Najeriya na fuskantar barazanar rugujewa

Archbishop na cocin Canterbury ta Ingila Dr. Rowan Williams ya yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar barazanar rugujewa a hannun 'yan kungiyar jama'atu ahlussunna lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram .

Shugaban cocin Ingila din ya kuma bukaci gwamnatin Burtaniya ta taimakawa Najeriya don kare mabiya wasu addinnan.

Kalaman na shugaban cocin sun yi dai dai da na tsohon jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, wanda shi ma ya yi hasashen rabewar kasar.

Masu sharhin al'amuran yau da kullum a Najeriya dai na ganin cewa matsalar da ke fuskantar kasar bata wargajewa ba ce, matsala ce ta rashin shugabanci mai nagarta.

Ita dai gwamnatin Najeriya ta sha bayyana cewa kasar tana nan a dunkule kuma babu abin da zai raba ta.

Karin bayani