Bom ya hallaka mutane tara a Somalia

Shugaban Somalia, Sheikh Sherif Ahmed Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani bam ya tashi a kusa da fadar Shugaban Kasar Somalia

'Yan sanda a Mogadishu babban birnin Somalia sun ce wani bam da aka dana a mota kuma aka tayar a kusa da fadar shugaban kasar ya kashe akalla mutane tara.

Jami'ai sun ce, bam din ya tarwatse ne a kusa da Muna Otel, wurin da akasarin lokuta 'yan siyasa da jami'an gwamnati ke ganawa.

Wani mutum mai suna Mohammed Irre ya ga lokacin da bam ya tarwatse kuma ya shaidawa BBC cewa suna zaune lokacin da bam din ya fashe wanda kuma ya girgiza duk fadin yankin.

Kungiyar nan ta masu tsattsauran ra'ayin Islama, Al-Shabab dai ta tabbatar wa da BBC cewa ita ce ta kai harin, amma ta musanta rahotannin farko da ke cewa ta yi amfani ne da dan kunar bakin-wake ne.

Karin bayani