An kashe wani Janar na soja a Syria

Sojojin Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojojin Syria

Gwamnatin Syria ta ce wadansu 'yan bindiga sun hallaka wani janar na soja.

A cewar kamfanin dillancin labarai na kasar ta Syria, an bindige Birgediya-Janar Issa al-Khouli ne a gaban gidansa da ke birnin Damascus.

Kamfanin dillancin labaran ya ce, wadansu 'yan ta'adda ne su uku dauke da bindigogi suka hallaka Janar Al-Khouli.

Janar Al-Khouli dai jami'in kiwon lafiya ne, kuma shi ne daraktan wani asibitin soja a birnin na Damascus.

Ko da yake a 'yan makwannin nan an hallaka jami'an soja masu yawa, wadanda ke da mukami irin na Janar Al-Khouli a fadace-fadacen da ake yi, an yi amannar cewa wannan ne karo na farko da aka yiwa wani jami'in soja kisan gilla a birnin na Damascus, tun lokacin da aka fara bore a Syriar, kusan shekara guda ke nan.

Kisan nasa na tuni da abin da aka kwashe shekaru ana yi a makwabciyar kasar, Iraki, har ya zuwa wannan lokacin.

Rahotanni sun ce jami'an Amurka sun yi amannar cewa 'yan kungiyar Al-Ka’ida reshen kasar Iraki ne ke kai hare-haren bam na kwanan nan wadanda ake kaiwa birnin Damascus ta hanyar amfani da motoci.

Idan har hakan ne, to kuwa hare-haren, da kuma kisan gillar da aka yiwa Janar Al-Khouli, za su kasance wata mummunar alamar da ke nuna cewa Al-Ka’ida ta shiga boren neman kawar da gwamnatin Syria.

Yawancin 'yan adawa a kasar ta Syria, wadanda suka kwashe wata da watanni suna fafutukar ganin cewa zanga-zangar ta kasance ta lumana, ba za su yi na'am da matakin da kungiyar ta Al-Ka’ida ke dauka ba.

'Yan gwagwarmaya a Syria sun zargi gwamnatin kasar da shirya hare-haren da aka kai a baya-bayan nan, don dai kawai a ce boren da ake yi aikin ta'addanci ne.

Karin bayani