Kayan da China ke fitarwa kasashen waje sun ragu

Wata masana'anta a China Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata masana'anta a China

Wasu alkaluma na baya- bayan nan sun nuna cewa adadin kayyakin da kasar China ke fitarwa ya ragu da digo biyar cikin dari idan aka kwatanta da bara.

Wannan shine karon farko cikin shekaru biyu da adadin kayyakin da kasar China ke fitarwa da kuma shigowa da su cikin gida suka ragu.

Hakan a cewar masana tattalin arziki baya rasa nasaba da fargabar da ake yi cewa China na fuskantar koma baya ta fuskar tattalin arziki.