An sanyawa Girka sharadi kan ceton tattalin arzikinta

Jean claude juncker da venizoles Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban tarayyar Turai, Jean Claude Juncker da ministan kudin Girka Evangelos Venizelos

Ministocin kudin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai sun gindaya wasu sharudda uku da ya kamata kasar Girka ta cika, kafin su amince a baiwa kasar karin Euro biliyan dari da talatin don ceto tattalin arzikinta.

Sharuddan sun hada da tilatawa majalisar dokokin kasar Girka ta amince da wani shirin tsuke bakin aljihu da zabtare miliyoyin Euro na kudaden da gwamnati ke kashewa, kana kuma sai shugabannin jam'iyun siyasa na kasar sun bada tabbacin cewa za su mutunta yarjejniyar bayan an gudanar da zabe.

Kwamishinan kungiyar mai kula da harkokin kudi da tattalin arziki, Olli Rehn ya bayyana cewa su na duba shawarar da Jamus da faransa suka bayar na kebe wani asusu ga Girka.

Saboda hakan wata hanya ce da za su iya sa ido sosai don tabbatar da an aiwatar da shirin ceton Girka.