An sake cafke Kabiru Sokoto

Kabiru Sokoto Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An ce shi babban jami'i ne a kungiyar ta Boko Haram

Jami'ai a Najeriya sun sake cafke Kabiru Sokoto, wanda ya kubuce daga hannun 'yan sanda bayan an zarge shi da kitsa harin bam kan wani coci a garin Madalla.

Shi dai Kabiru Sokoto ya kufce ne daga hannun jami'an tsaro bayanda aka kama shi.

Ana dai zarginsa ne da shirya harin ranar Kirismeti da kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kaiwa a garin Madalla da ke kusa da Abuja babban birnin Najeriya wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama.

Shi dai mutumin da hukumar leken Asirin Najeriya SSS din ta ce shi ne Kabiru Sokoto yayi kama da wanda kafofin yada labarai suka nuna hotonsa a baya a matsayin wanda aka ce ya kubce daga hannun jami'an tsaro.

Wakilin BBC Muhammad Abba a Abuja, ya tambaye shi ko shi ne Kabiru Sokoto, inda kuma ya amsa cewa shi din ne, kuma ya fito ne daga garin Sokoto a Arewa maso Yammacin Najeriyar.

'A shirye muke'

An tsaurara matakan tsaro a cikin da kewayen hukumar ta SSS, inda sojoji dauke da bindigogi suke wa mutumin da aka kama din rakiya.

Hukumomin tsaron dai ba su bayar da cikakken bayanin yadda suka kama shi ba, sai dai sun ce babu wani mai aikata miyagun laifuka da zai tsere wa hukumomi.

"A shirye muke mu kawo karshen ayyukan tsirarun miyagun mutane", a cewar Marilyn Ogar mai magana da yawun hukumar SSS.

"Muna kuma gargadin cewa, babu mafaka ga duk masu aikata miyagun laifuka a duk inda suke", a cewarta.

Shi dai Kabiru Sokoto wanda aka kama a garin Mutum Biu da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba, tserewar da ya yi daga hanun jami'an 'yan sanda na daga cikin dalilan da suka gaggauta murabus din tsohon sufeto janar na 'yan sandan Nigeria.

A cewar hukumar tsaron ta SSS, an haifi Kabiru Sokoto ne a ranar 9 ga watan Mayun shekarar 1983.

Kuma ya yi makarantun Firamare da Sakandare da makarantar koyon aikin unguwarzoma a jihar Sokoto.

Hukumar ta ce shi ne ya shirya ziyarar da tsohon shugaban kungiyar Jama'atu Ahlissuna Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram wato Muhammad Yusuf ya kai a jihar ta Sokoto a shekarar 2009, wanda ya kaiga nada shi a matsayin shugaban kungiyar a jihar ta Sokoto.

Hukumomin tsaron sun baiwa manema labaru takaitacciyar damar tambayarsa sunansa.

A halin yanzu dai hukumar ta SSS ta ce bayan kammala bincikenta za ta gurfanar da shi a gaban kuliya.

Karin bayani