An fara biyan diyya game da harin Bam na Madalla

Wasu masu alhinin mutuwar 'yan uwansu a harin Madalla

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wasu masu alhinin mutuwar 'yan uwansu a harin Madalla

A Nigeria, gwamnatin Jihar Naija ta fara biyan diyya ga wadanda harin bam ya rutsa da su a kusa da wata majami'a da ke garin Madalla a karamar hukumar Suleja.

Sakataren Majami'ar, Father Gadaci, ya tabbatarwa BBC cewa jami'an gwamnatin sun ziyarce su sau biyu, kuma sun mika cakin kudi ga wasu daga cikin iyalan da suka rasa 'yan uwansu.

A ranar Kirsimatin bara ne dai bam ya tashi a kusa da majami'ar Katolika ta St. Theresa, ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da arba'in yayin da wasu da dama suka jikkata.

Kungiyar jama'atu Ahlul sunna lil da'awati wal jihad ko Boko Haram ce ta dauki alhakin kai harin.