Sudan da Sudan ta kudu za su tsagaita wuta

Taswirar jamhuriyar Sudan da kuma kasar Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Taswirar jamhuriyar Sudan da kuma kasar Sudan ta Kudu

Gwamnatin Jamhuriyar Sudan da kuma kasar Sudan ta kudu sun rattaba hannu akan wata yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakaninsu.

Kungiyar tarayyar Afrika ce ta shiga tsakani aka cimma yarjejniyar da nufin kawo karshen tashe tashen hankulan kan batun albarkatun man fetur.

Shugaban kasar Afrika ta kudu Thabo Mbeki, wanda shine babban mai shiga tsakanin ya shaidawa manema labarai cewa yarjejeniyar da aka cimma za ta taimaka wajen hana ci gaba da tashe tashen hankula tsakanin bangarorin biyu.