'Yan sanda da masu zanga zanga sun kara a Girka

Tashin hankali a Girka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tashin hankali a Girka

A kasar Girka 'yan sanda da masu zanga zanga sun yi taho-mu-gama a gaban majalisar dokoki a birnin Athens, yayin da 'yan majalisar ke yin muhawara a kan sabbin matakan tsuke bakin aljihun gwamnati.

'Yan sandan sun harba wa masu zanga zangar barkonon tsohuwa, yayin da su kuma ke jifansu da duwatsu da bama baman petur.

An kona gine gine da dama.

Nan da 'yan sa'o'i ne ake sa ran cewa, majalisar dokokin Girkan za ta kada kuri'a a kan sabbin matakan rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa.

Hakan yana daga cikin sharuddan da ya kamata kasar Girkar ta cika, kamin ta sami kudaden belin da suka kai biliyoyin dalar Amirka daga Tarayyar Turai da asusun bada lamunin IMF.

Karin bayani