Za'a buga wasan karshe a gasar cin kofin Afrika

A yau ne za'a kammala gasar cin kofin kwallon kafa ta Afrika da akeyi a kasashen Gabon da Equatorial Guinea, inda kasar Zambia za ta fafata da kasar Ivory Coast a wasan zagayen karshe.

A wasan da aka buga a daren jiya tsakanin Ghana da Mali a zagayen kusa da na karshe, Malin ta lallasa Ghana da ci biyu babu ko daya.

Abinda ya kai Mali zama kasa ta uku a gasar baki daya.