Shugaban tawagar Larabawa a Syria yayi murabus

Janar Mohammed Al-Dabi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Janar Mohammed Al-Dabi

Shugaban tawagar kungiyar kasashen Larabawa mai sa ido a kan tashin hankalin da ke faruwa a Syria, yayi murabus.

Murabus din Janar Mohammed Al-Dabi ya zo ne a ranar da kungiyar ke yin taro, domin tattaunawa akan batun aika wata sabuwar tawagar hadin guiwa tare da Majalisar Dinkin Duniya, zuwa Syriar.

An bada shawarar cewa, a nada ministan harkokin wajen Jordan, Abdel Illah Khatib, a matsayin wanda zai zama wakilin kungiyar kasashen Larabawa a Syria a nan gaba.

Kungiyar ta janye tawagar masu sa-idonta a watan da ya wuce, yayin da gwamnatin Syriar ke cigaba da murkushe boren da ake, na neman kawar da shugaba Bashar Al-Assad.

Karin bayani