'Talauci ya fi yawa a jihar Sakkwato'

Sokoto
Image caption Wasu matalauta a Najeriya

Talauci a Najeriya ya yi matukar karuwa inda kusan mutane miliyon dari daya ke rayuwa a kasa da dalar Amurka daya a kullum.

Wadannan alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar ta fitar a ranar Litinin sun nuna cewar yawancin 'yan Najeriya na cikin tsananin talauci saboda basa iya mallakar wajen zama ko kuma abincin ci ko rigunan sawa.

A cewar hukumar, talaucin ya karu daga kashi hamsin da hudu da digo bakwai a cikin dari a shekara ta 2004, inda ya koma kashi sittin da digo tara a cikin dari a shekara ta 2010.

Haka kuma rahoton ya nuna cewar arewa maso yamma da kuma arewa maso gabas sune kan gaba a karuwar talaucin a fadin Najeriya a yayin da jihar Sakkwato tafi kowacce jiha a kasar yawan matalauta.

Koda yake dai ana hasashen cewar tattalin arzikin kasar zai cigaba da bunkasa, amma kuma akwai alamun cewar talauci zai kara yawa a tsakanin al'umma inda tazara za ta karu tsakanin masu kudi da matalauta

Shugaban hukumar kiddiddiga ta kasar Yemi Kale ya ce "Duk da irin habakar tattalin arziki da za a samu a kasar amma dai talauci zai dinga karuwa a kowacce shekara".

Masu sharhi sun yi tsokaci

"Wannan kiyasin bai kai yadda al'amura suke a kasa ba", a cewar Dokta Hussani Abdu, na kungiyar bayar da agaji ta ACTIONAID a Najeriya.

Ya ce miliyoyin jama'a na fama da talauci a kasar, kuma mahukunta ba sa yin abinda ya kamata wurin shawo kan matsalar.

"Yawancin jama'a manoma ne kuma wajibi ne gwamnati ta tallafa musu idan ana son a fitar da su daga kangin talauci," a cewar Hussaini Abdu.

Cin hanci da rashawa sun yi wa tattalin arzikin Najeriya katutu, inda 'yan siyasar kasar, cikin shekaru masu yawa suka maida hankali wajen azurta kansu a maimakon gina hanyoyi da samarda ayyukan yi a yayinda kasar ke hako gangar danyen mai miliyon biyu a kullum.

Karin bayani