Jama'a a Somalia na goyan bayan Al Qaida

'Yan kungiyar Al Shabaab Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan kungiyar Al Shabaab

Mutane dubu biyu ne suka shiga cikin wani gangami a Somalia da kungiyar 'yan gwagwarmayar Islaman nan ta Al-Shabaab ta shirya.

Wani wakilin BBC a Somalia ya ce masu zanga zanga sun bayyana goyon bayansu ga kumgiyar Al-Qaeda -- wadda al-Shabaab ta ce ta kulla kawance da ita.

Har ila yau gangamin sun nuna rashin jin dadi game da taron kasa da kasar da za a yi a Somalia a nan London nan gaba a cikin watan nan.

Gwamnatin rikon kwaryar Somalia dai na yakar al-Shabaab don neman iko da kudanci da kuma tsakiyar Somalia.

Karin bayani