Navy Pillay ta soki gwamnatin Syria

Navy Pillay Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Navy Pillay

Kwamishiniyar hukumar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya, Navi Pillay ta kaddamar da kakkausan suka akan gwamnatin Syria a zauren majalisar dinkin duniya.

Inda tace gazawar da kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya yi na daukar tsayayyen mataki akan abinda ke faruwa a Syria ya karawa gwamnatin kasar karfin gwiwar farwa jama'ar kasar da nufin murkushe boren da ake yi.

Kwamishiniyar ta kuma ce, jinkirta daukar matakin kasashen duniya akan lamarin na Syria zai, kara tsananin halin da 'yan kasar suke ciki.

Karin bayani