'Yan adawa na shirin yin zanga- zanga a Bahrain

Masu zanga- zanga a Bahrain Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga- zanga a Bahrain na yunkurin sake mamaye sha- tale- talen Pearl dake birnin Manama

Jami'an tsaro a Kasar Bahrain sun harba hayaki mai sa hawaye da gurnetin da zai tarwatsa masu zanga-zanga a ranar jajiberin cika shekara daya da zanga- zangar neman kafa demokradiyya a Kasar ta larabawa.

Dubban masu zanga-zangar na kokarin mamaye sha-tale-talen dake tsakiyar babban birnin Kasar Manama, wurin da aka gudanar da zanga-zangar a bara.

Mafi rinjayen masu zanga-zangar dai 'yan Shi'a ne wadanda ke neman kafuwar gwamnatin demokradiyya a Kasar wadda 'yan Sunni ke jagoran ta.

Gwamnatin Sarki Hamad bin Isa Al Khalifa ta yi alkawarin gudanar da wasu sauye sauye na siyasa da kuma a bangaren 'yan sandan Kasar.

Amma 'yan adawa mafiyawanci 'yan Shi'a cewa suke gwamnatin ba ta tabuka komai ba, su na masu cewar za su fito zuwa sha-tale- talen a wani mataki na kalubalantar masarautar ta Bahrain kai tsaye

Karin bayani