China zata ceto tattalin arzukin nahiyar Turai

Shugabannin tarayyar Turai sun isa China Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugabannin tarayyar Turai sun isa China

Shugabannin kasar China sun fadawa jami'an gwamnatocin kasashen Turai dake ziyara kasar cewa, gwamnatin Chinar na da aniyar tallafawa Turai domin fita daga cikin rintsin bashin da ta afka.

Tawagar tarayyar turan ta bukaci China da ta sa kudi a wani asusun tallafi ga kasashen turan da bashi ya yi wa katutu.

Sai dai kuma duk da hakan Praministan Chinan, Wen Jiabao bai furta alkawarin wasu kudade da Chinan zata ba kasashen turan.

A farkon makon nan Praminsta Jiabao ya ce kasarsa na tunanin kara kudin taimakon da take bayar wa, ta hannun hukumar bada lamuni ta duniya.

A nasa bangaren kuma shugaban kungiyar tarayyar Turai, Herman Van Rompuy ya ce China da kungiyar tarayyar Turai sun dukufa wajen karfafa dagantaka tsakaninsu saboda yin hakan na da muhimmanci sosai ga wannan zamani.

Karin bayani