Moody's ta rage darajar karfin tattalin arzikin Burtaniya da Faransa

Firayim Ministan Burtaniya David Cameron Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Nahiyar Turai na fuskantar matsalar rikicin tattalin arziki

Wata hukumar da ke auna karfin iya biyan bashin Kasashe ta rage darajar da ake kallon Burtaniya da Faransa na da ita ta fuskar tattalin arziki.

Hukumar ta Moody's ta rage darajar Kasashen biyu ne saboda damuwar da ake da ita a kan ko za su iya jure raunin tattalin arzikin da ya shafi nahiyar Turai a dalilin basussuka.

Haka nan kuma hukumar ta sassauta kudin ruwan da za a caji wasu kasashen Turai shida wadanda suka hada da Italia da Portugal da kuma Spaniya.

Hukumar ta Moody's tace sauye-sauyen na ta ya yi la'akari ne da hangen da ake yi na kuncin tattalin arziki da kasashen Turai za su iya fuskanta da kuma rashin tabbas da ake da shi na hanyoyin da za a samu kudin da za a iya warware basussukan da suka dabaibaye nahiyar.

Karin bayani