Gobara ta hallaka fursunoni fiye da 300 a Honduras

Gobara a Honduras Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gobara a Honduras

Shugaba Porfirio Lobo na Honduras ya dakatar da jami'an da ke kula da wani kurkuku na kasa daga bakin aikinsu.

Ya ce ba za su koma bakin aiki ba har sai an gano wanda ke da alhakin aukuwar wata gagarumar gobarar da ta barke a daren jiya, a gidan yari na Comayagua, kamar kilomita 80 arewa da Tegucigalpa, babban birnin kasar.

Fursunoni fiye da 300 ne suka hallaka.

Gobarar ta kuma jikkata wasu 'yan kason da dama.

Ya zuwa yanzu babu tabbaci akan ko me ya haddasa wannan gobara.

Amma kuma wasu jami'ai sun ce matsalar wutar lantarki ce ta haddasa gobarar, yayin da wasu kafofin yada labarun kasar ke cewa, anyi tarzoma ne acikin gidan yarin.

Akwai dai 'yan fursuna fiye da dari takwas, kuma wani kakakin sashen kashe gobara Josue Garcia yace, ya ganewa idanunsa mummunan bala'i.

Karin bayani