'Yankin Sahel na bukatar agajin gaggawa don kaucewa yunwa'

Jagorar hukumar kula da ci gaba ta majalisar dinkin Duniya Helen Klark, ta bayyana cewa, ana bukatar dala miliyan dari bakwai da ashirin da biyar din ne domin biyan bukatun jama'ar da ke cikin mawuyacin hali sakamakon matsalar yunwa a wannan shekarar.

Hukumomin na majalisar dinkin duniya da ke taro yau a Rome, sun bayyana cewa akwai bukatar a yi tallagfin gaggawa ga miliyoyin jama'ar wadandda ke yankin Sahel kuma suke da matukar bukatar taimako, domin kaucewa al'amarin kafun ya zama gagarumar annoba.

Yankin na Sahel dai ya hada da bangarorin yammaci da kuma tsakiyar Afrika kudu da sahara kuma ya kunshi kasashe da dama da suka saba fuskantar matsalar karancin abinci.

Karancin ruwan sama

A shekarar da ta gabata, hukumar kula da abinci ta majalisar dinkin duniya, ta bayyana cewa kasashe da dama a yankin na Sahel sun fuskanci karancin ruwan sama a damaunar da ta gabata, kuma daukewar ruwan saman da wuri, ya janyo raguwar abincin da jama'ar yankin ke nomawa, abinda ya haifar musu da karancin abincin da ake fuskanta a yanzu.

Hukumomin da ke halartar taron sunhadar da IFAD, UNDP da kuma manyan jami'an tarayyar turai. Tuni dai tarayyar turan ta bayyana bada tallafin yuro miliyan talatin ga shirin samar da abinci na majalisar dinkin duniya domin tallafawa mata da kananan yara a yankin na sahel.

Hukumar ta majalisar dinkin duniya ta ce za ta yi amfani da tallafin domin samar da abinci mai gina jiki ga yara miliyan daya 'yan kasa da shekaru biyu a yankin sahel.

Dokar ta baci

Ya zuwa yanzu dai kasashe biyar a yankin na sahel da suka hada da Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritaniya da Nijar, sun bayyana dokar ta baci a kan matsalar abinci, suka kuma ayyana neman taimako daga kasashen duniya.

A gobe ne dai mataimakiyar sakatare janar na majalisar dinkin duniya mai kula da harkokin jin kai Valerie Amos za ta jagoranc wata tawaga zuwa jamhuriyar Nijar inda kimanin mutane miliyan biyar da dubu dari hudu ke fama da matsalar abinci.

Ana sa ran tawagar za ta gana da shugaban Nijar Muhammadu Isuhu, da fira minista Brigi Rafini.

Tun a watan satumbar da ya gabata ne dai majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa matsalar karancin abincin da ake fama da shi a yankin na Sahel ka iya gagarar kundila

Karin bayani