Miliyoyin yara za su tashi da nakasar jiki da ta kwakwalwa

Yaron da ke fama da rashin abinci mai gina jiki Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rashin isasshen abinci mai gina jiki na cigaba da yin barazana ga lafiyar kananan yara a Kasashe masu tasowa

Kungiyar ba da agaji ta 'Save the Children' ta bayyana cewa Yara miliyan dari biyar ne za su tashi da nakasar jiki da ta kwakwalwa a cikin shekaru goma sha biyar masu zuwa saboda rashin samun isasshen abinci mai gina jiki.

Kungiyar tace akwai bukatar kara tashi tsaye a taimaka don kawar da matsalar ta karancin abincin mai gina jiki a Kasashe matalauta.

Wani bincike da kungiyar ta 'Save The Children' ta gudanar a Kasashen India da Najeriya da Pakistan da Peru da Bangladesh ya gano cewar Iyalai da dama a Kasashen ba su da sukunin samun abubuwa irin su nama da madara ko kuma ganyayyaki masu gina jiki.

Kungiyar dai tayi amfani ne da hanyar hirarrakin da ta yi da jama'a wajen tattara bayanan ta a wadanan Kasashe cikin har da Najeriya, inda ta ce ta na daya daga cikin Kasashen da ake da kashi hamsin cikin dari na yaran da ke fama da rashin abinci mai gina jiki.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin Burtaniya da ta shirya wani babban taro akan batun yunwa, tana mai cewar yara 'yan kasa da shekaru biyu na matukar bukatar taimako.

Karin bayani