Najeriya za ta bude ofisoshin kula da tsaro a Nijar da Mali

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Najeriya za ta bude ofisoshin kula da tsaro a Mali da Nijar

Gwamnatin Najeriya za ta bude sabbin ofisoshin kula da tsaro a Kasashen Nijar da Mali a yunkurin ta na maganin matsalar Boko Haram.

Hukumomin Kasar sun ce za a bude ofisoshin ne domin su rika aiki kafada-da-kafada da jami'an tsaron kasashen biyu da nufin kare duk wata barazanar tsaro a tsakanin Kasashen.

Gwamnatin Najeriyar ta mikawa majalisun dokokin Kasar kasafin kudin da za a gudanar da ofisoshin biyu, wadanda za su kasance da mazauni a Niamey da Bamako.

Kasashen Nijar da Mali dai na fama da matsalolin tabarbarewar tsaro sakamakon ayyukan da kungiyar Al-Qaeda reshen Magrib ke gudanarwa.

Honourable Isa Mohammad Ashiru shi ne mataimakin Shugaban kwamatin tsare-tsare na majalisar wakilan Najeriya, ya kuma shaidawa BBC cewar za a rinka musayar bayanai da wadannan Kasashe domin dakile matsalolin tsaron da ake fama da su.

Karin bayani