Majalisar Dattawa ta amince da Lamurde

Majalisar Dattawa ta amince da Lamurde Hakkin mallakar hoto google
Image caption Dama dai Lamurde babban jami'i ne a hukumar ta EFCC

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da Ibrahim Lamurde a matsayin shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC.

Lamurde ya maye gurbin tsohuwar shugabar hukumar Farida Waziri wacce aka kora daga aiki a watan Nuwamban bara.

Hakan ne kuma ya sa shugaba Goodluck Jonathan ne ya nada Mr Lamurde - wanda babban jami'i ne a hukumar domin shugabantar EFFC na wucin-gadi.

Amma daga bisani ya mika sunansa ga Majalisar dattawan domin neman amincewarta kan Mr Lamurde ya jagoranci hukumar a matsayin shugaba na din-din-din.

Karin bayani