Taron Shugabannin Kasashen Kungiyar ECOWAS

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Shugabannin Kasashen Kungiyar za su tattauna matsalar tsaro a taron su na yau

Shugabannin Kasashe na Kungiyar raya tattalin arzikin Afrika ta Yamma ECOWAS za su fara wani taron kwanaki biyu nan gaba a yau a Najeriya.

Shugabannin Kasashen za su tattauna matsaloli da dama da ke damun yankin, batun da ya hada da rashin tsaro sakamakon dubban makaman da suka fito daga Libya .

Shugabannin na Kasashe goma sha-biyar za kuma su tattauna hanyoyin da za a rinka musayar bayanai na sirri a tsakaninsu da kuma hanyoyin da za su bi na kawo karshen safarar makamai tsakanin Kasashen da kuma kara tamke damarar tsaro a kan iyakoki.

Haka nan kuma taron kolin zai duba batun 'yan gudun hijira da fashin da ake yi a gabar teku ta yammacin Afrika.

Ana kuma sa ran za a zabi sabon Shugaban Kungiyar ta ECOWAS a ranar juma'a.

Karin bayani