An yankewa Abdulmutallab hukuncin daurin rai-da-rai

mutallab Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lamarin ya faru ne a ranar kirsimetin shekara ta 2009

Wata kotu a Amurka ta yankewa dan Najeriya Umar faruk Abdulmutallab hukuncin daurin rai-da-rai, bayan da aka same shi da kokarin tayar da bam a wani jirgin saman Amurka.

Umar Farouk Abdulmutallab, dan shekaru 25, ya amsa laifin yunkurin tarwatsa wani jirgin saman kasuwanci na Amurka, a wani lamari da ake ganin yunkurin kunar bakin wake ne.

Abdulmutallab ya kone sosai lokacin da bam din da ya boye a kamfansa ya kasa tashi gaba daya, kamar yadda masu gabatr da kara suka ce.

Akalla mutane 300 ne a cikin jirgin wanda ya taso daga Amsterdam na kasar Holland zuwa birnin Detroit na Amurka.

Umar Faruk Mutallab wanda mahaifinsa Abdulmutallab, shahararren dan kasuwa ne kuma ma'aikacin banki, ya fuskanci tuhuma kan laifuka takwas da suka hada da ta'addanci da kuma kisan gilla.

Kungiyar Al-Qaeda a yankin Larabawa da ke da hedkwata a kasar Yemen, ta ce ita ce ta dauki shirya harin.

Danginsa sun koka

Sai dai danginsa sun koka kan yadda mahukunta a Amurka suka yi watsi da hujjojin da lauyoyin Abdulmutallab suka gabatar.

"Muna kira ga sashen shari'a na Amurka da su sake yin nazari akan hukuncin daurin rai-da-ran da aka yankewa Umar Faruk Muttalab", a cewar sanarwar iyalin Alhaji Umar Mutallab da suka fitar.

Haka nan kuma iyalan sun yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta ci gaba da goyan bayan da ta ke bayarwa wajen tuntubar gwamnatin Amurka domin tabbatar da an sake yin nazari akan shari'ar domin yin la'akari da hujjojin da lauyoyin Umar Faruk Muttalab din suka gabatar a gaban kotun.

Babu tabbas ko Umar Faruk Abdulmutallab zai daukaka kara kan hukuncin ko kuma a'a.

Karin bayani