An kai hari kan wani gidan yari a Najeriya

An kai hari kan wani gidan yari a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumomi sun ce sun kame fursunoni 20 daga cikin 119 da suka tsere

Hukumomi a Najeriya sun ce sun kame fursunoni 20 daga cikin 119 da suka tsere bayan da 'yan bindiga suka kai hari da bama-bamai da bindigogi kan wani gidan yari a Jihar Kogi da ke tsakiyar kasar, inda suka kubutar da 'yan fursuna fiye da dari.

Jami'ai sun ce cikin wadanda suka tsere na zaman jiran shari'a ne, kuma babu wani mai babban laifi a cikinsu.

'Yan bindigar dai sun harbe jami'in gidan yarin guda.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki nauyin wannan harin, amma tuni aka fara tunanin ko kungiyar Boko Haram ce, ganin cewa a baya kungiyar ta kai hare-hare makamantan wannan a jihar Bauchi.

A wancan lokacin kungiyar ta kubutar da fursunoni kusan 700, yawancinsu 'ya'yan kungiyar.

Sakacin jami'an tsaro

Sai dai kakakin hukumar gidan yarin ta Jihar Hadiza Aminu, ta shaida wa BBC cewa ba sa zargin Boko Haram a harin da aka kai a gidan yarin na garin Koton-Karifi, mai nisan kilomita 160 daga Abuja babban birnin kasar.

Rahotannin farko sun ce yan fursuna 199 ne suka tsere, amma daga bisani hukumomi sun rage adadin.

Wani jami'in 'yan sanda da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa wata jarida a Najeriya cewa kimanin 'yan bindiga 20 ne akan babura suka kai hari kan gidan yarin.

Ya kara da cewa sun shafe kimanin mintina 30 suna kaddamar da harin.

Masu nazarin al'amura na ganin ko ma dai su wanene suka balla gidan yarin akwai yiwuwar sakaci daga jami'an tsaro.

Karin bayani