Shirin IFAD na taimakawa makiyaya a Najeriya

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Asusun IFAD na wani shiri na kawo wasu nau'in ingantattun shanu a Najeriya

Asusun bunkasa ayyukan gona na duniya, IFAD, na gudanar da wani shiri ne na raba wa makiyaya wasu nau'in ingantattun shanu don yada iri da nufin samar da karin madara da nama, don kare kwararowar matsalar rashin abincin.

Kasashen dake yankin Sahel a yammacin Afirka dai na cikin matsalar yunwa sakamakon rashin abinci.

Hakan ya sa Majalisar dinkin duniya da kuma Kungiyar Kasashen Turai suke neman a tallafawa Kasashen don ceto su daga matsalar.