Zaben Shugaban kasa a Masar ya shiga rudu

Sabbin @Yan majalisar dokokin Masar Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sabbin @Yan majalisar dokokin Masar

Mahukuntan kasar Masar sun gaza cimma matsaya game da ranar da za a yi zaben shugaban kasa na farko a bayan mulkin Mubarak.

Shugaban kotun tsarin mulkin kasar Farouk Sultan ya ce kwamitin ya zauna ya kuma yanke shawarar dage bayyanatsarin lokacin gudanar da zaben har sai an samu daidaito.

Shugaban Hukmar zaben ta Masar ya bayyana haka ne wa wajen wani taron manema labarai da a da ya kiran don bayyana tsarin lokacin zaben Shugaban kasa.

Sai dai ya ce yana fatan za a kammala tafiyar da dukanin shirin a karshen watan Mayu.

A cikin 'yan kwanakin nan dai wasu jami'an gwamnati 2 sun bayar da ranaku 2 daban daban -- daya yana cewar za a yi zaben a cikin watan Mayu , dayan kuma ya ce, a cikin watan Yuni.

Rudanin ya nuna irin rarrabuwar kawunan da ake ta ita a bayan fage, watakila game da sharadin mika mulki ga farar hula, Saboda da zaran an yin zaben Shugaban kasa, ana sa ran soji su saki mulki su koma barikokinsu.

Karin bayani