'Iran na fadada shirinta na nukiliya'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ma'aikatan makamashin nukiliya a Iran

Jami'an diflomasiyya a Vienna, babban birnin kasar Austria, sun ce Iran tana wani gagarumin yunkuri na fadada shirinta na nukiliya a wani wuri da ke karkashin kasa a birnin Qum.

A cewar jami'an, kasar ta Iran tana shirin girke dubban sababbin na'urorin inganta makamashin uranium a masana'antar, inda tuni aka kakkafa muhimman kayayyakin da ake bukata don tallafawa shirin.

Jami'an sun ce wadannan na'urori za su iya taimakawa sosai wajen hanzarta samar da ingantaccen makamashin uranium wanda za a iya amfani da shi don kera makamin na nukiliya.

Ko da a makon jiya ma, sai da Shugaba Mahmoud Ahmadinejad ya ce nan da 'yan kwanaki ne kasarsa za ta ba da sanarwa a kan gagarumin ci gaban da ta samu ta fannin nukiliya.

Ya kuma ce masana kimiyyar kasar za su taka rawa sosai a wannan al'amari.

Sai dai ya kara da cewa Iran na sarrafa makamashin ne don ta iya biyan muhimman bukatunta.

Kasashen Yammacin duniya, wadanda tuni suka kakabawa Iran din takunkumi, sun zarge ta da yunkurin kera makamn nukiliya, amma kuma ta tsaya kai da fata cewa shirin nata na samar da wutar lantarki ne.

A wannan makon ne dai masu sanya ido daga Majalisar Dinkin Duniya ke shirin sake zuwa kasar ta Iran, don tattaunawa da hukumomi kan fargabar da ake yi game da shirinta na kera makamin nukiliyar.

Karin bayani