Bam ya tashi a Suleja

Wata barnar da bam yayi a Suleja Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wata barnar da bam yayi a Suleja

Wani abu da ake jin bam ne ya tashi a wata unguwa dake garin Suleja na jihar Neja dake arewacin Najeriya.

Bam din ya jikkata mutane biyar da kuma lalata motoci biyar.

Wasu rahotanni sun ce bom din ya tashi ne a kusa da wani Otel yayinda ake gudanar da wasu taruka na karshen mako.

Hukumar bada Agajin Gaggawa ta kasar, NEMA, tace ta garzaya da wadanda suka jikkatan zuwa asibiti.

Rundunar Yansandan jihar Naijar ta tabbatar da abkuwar lamarin, suka ce wani mutum ne ya bar bam din a cikin wata mota, yanzu haka kuma suna ci gaba da bincike kan lamarin.

Karin bayani