'Takunkumi na yin tasiri a kan Syria'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga-zanga a Syria

Wani fitaccen dan kasuwar Syria, Faisal al-Qudsi, ya ce takunkumin da aka sanyawa kasar yana durkusar da tattalin arzikinta, kuma Shugaba Bashar al-Assad da gwamnatinsa ba za su wuce watanni shida a kan mulki ba nan gaba.

Faisal al-Qudsi, wanda da ne ga wani tsohon shugaban kasar ta Syria, ya shaidawa BBC cewa takunkumin hana fitar da man fetur da kuma durkushewar bangaren yawon bude ido ya rage yawan arzikin da ke kai komo a kasar da kusan kashi arba'in da biyar cikin dari.

''Na ba gwamnatin watanni shida, matakin sojin da take dauka zai kawo karshe, saboda sojojin sun fara gajiya, kuma ba inda matakin ya kai mu. Wajibi ne bayan wata shida su hau teburin shawarwari ko kuma su daina kashe mutane. Da zarar sun daina kisa kuma yawan masu zanga-zanga zai karu'', in ji Mr Al-Qudsi.

Rikici ya barke a Damascus

Mummunan rikici ya barke a Damascus, babban birnin kasar ta Syria ranar Asabar, inda wata tawagar diflomasiyya daga kasar China ke kokarin sasanta tsakanin Shugaba Assad da abokan hamayyarsa, masu zanga zanga.

Jana'izar wasu masu zanga-zanga da aka kashe a yammacin Damascus ta rikide zuwa daya daga cikin manyan zanga-zangar da aka taba gani a birnin.

Masu fafutuka sun ce an kashe akalla mutun daya a lokacin da dakarun tsaro suka bude wuta.

A waje daya kuma wani wakilin gwamnatin China ya yi kira ga 'yan tawaye da dakarun gwamnatin Syrian da su dakatar da rikicin.

Zhai Jun ya ce gwamnatin China na goyon bayan shirye-shiryen gwamnatin Syria na yin kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da sauye sauyen da zaa yiwa kundin tsarin mulkin kasar.

Karin bayani