Korea ta Kudu ta yi atisayen soji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Korea ta Kudu a lokacin da suke atisaye

Korea ta Kudu ta gudanar da wani atisaye na soja wanda aka yi amfani da harsasai masu rai a kusa da kan iyakarta da Korea ta Arewa, duk kuwa da gargadin da Arewan ta yi da kada a yi atisayen.

Atisayen dai ya kunshi barin wuta da makaman atilare da igwa da kuma jiragen saman yaki masu saukar ungulu.

Jami'an Korea ta Kudu sun ce atisaye ne da aka saba yi, amma rundunar sojan Korea ta Arewa ta ce takalar fada ce.

Kakakin gwamnatin Korea ta Kudu, Kim Hyung Suk, ya ce, ''Wannan atisaye ne da aka saba yi, kuma a yankin kasarmu, saboda tsaron kasa. Don haka kalaman na Korea ta arewa ba su dace ba''.

An umarci mazauna yankin su fice

Korea ta Arewa ta shawarci 'yan Korea ta Kudu mazauna yankin da su fice.

Duk da yake Korea ta Arewa ta sha yi wa makwabciyarta ta Kudu gargadi idan tana gudanar da irin wannan atisaye, amma ba kasafai ta ke gargadi ga 'yan kasar da ke garuruwan kusa da kan iyaka, su kauracewa yankin ba.

Daruruwan mazauna yankin ne dai suka fice zuwa wasu gidaje da ke da kariya daga bama-bamai, sa'oi biyu gabanin Koriya ta Kudu ta fara atisayen.

A watan Nuwanban shekarar 2010, Korea Ta Arewa ta yi luguden wuta a kan tsuburin Yeon-pyong, inda mutane hudu suka mutu, kana da dama suka samu raunuka.

Harin dai shi ne irin sa na farko da Korea ta Arewa ta kai kan Korea ta Kudu tun bayan yakin da kasashen biyu suka yi.

Karin bayani