Farashin kayayyaki ya hau a Najeriya

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, wani rahoton da Hukumar Kididdigar kasar ta fitar na nuna cewa, an samu hauhawar farashin kayan abinci da na wasu abubuwa da suka shafi sufuri a kasar, a watan Janairun wannan shekarar.

Rahoton dai ya danganta hauhawar farashin ne ga janye tallafin da gwamnati ta yi a bangaren man fetur.

Wannan dai shi ne rahoto na farko ta fuskar farashi da hukumar kididdigar ta fitar tun bayan janyen tallafin man fetur da gwamnatin Najeriyar ta yi a wannan shekarar.

Karin bayani