Sudan ta kudu za ta tsuke bakin aljihunta

Sudan ta kudu za ta tsuke bakin aljihunta Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sudan ta kudu ta dade tana fama da matsaloli tun bayan da ta samu 'yancin kai

Sudan ta kudu tace za ta tsuke bakin aljihunta ta hanyar rage rabin kudaden da take kashewa, amma lamarin ba zai shafi kudaden da ake kashewa wajen biyan albashi ba.

A watan da ya gabata ne dai sabuwar kasar ta dakatar da fitar mai zuwa kasauwannin duniya saboda sabani tsakaninta da Jamhuriyar Sudan.

Da yake mai ne dai ke samar kusan dukkan kudin shigar gwamnatin kasar Sudan ta kudu, a yanzu wasu masana tattalin arziki na tunanin ko yaya al'amura za su kasancewa Sudan ta Kudun.

Wannan labari ne mai dadin ji ga dubun dubatar ma'aikatan gwamnati dama jami'an tsaro maza da mata.

Babu ma'aikacin da lamarin zai shafa a ma'aikatar harkokin Kudi albashin su zai ci gaba da kasancewa yadda yake, amma zai shafi wasu sauran fannonin.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu

Haka ma adadin kudaden da aka tura zuwa ko daukacin jihohi goma na Kudancin Sudan din suma za a rage su, kodayake ba zai zama mai yawa ba kamar yadda gwamnatin tace.

Har yanzu dai babu takamaiman kiyasi a kasa, amma da alamu me yiwuwa matakin zai maye gurbin asarar da kasar tayi a bangaren kudaden shigar da akan samu daga bangaren man wanda shi ne kashi casa'in da takwas bisa dari na kasafin kudin Sudan ta Kudun.

Sudan ta kudun dai na fitar na fitar da man nata ne ta hanyar amfani da tashoshin ruwan makwabciyar ta Sudan bayan da ta samu galabar cin gashin kanta a cikin watan Yulin shekarar da ta gabata.

Sai dai daga bisani ne kasar Sudan ta fara kame man na Sudan ta Kudun sakamakon abinda tace na rashin wata cikakkiyar yarjejeniyar yadda kasar Sudan ta Kudun za ta rika biyan kudin fito.

Bayan da sabuwar kasar ta rufe ayyukan hakar man nata, shugaban kasar Sudan Omar Albashir ya mayar da martain cewar lallai ana nesa-nesa da samun zaman lafiya.

Duk da haka a halin da ake ciki tasirin rufe matatun man ya shafi daukacin fannonin tattalin arziki, domin Kudancin Sudan na bukatar kudaden shiga daga danyen man da ta saba fitarwa, kana kuma Sudan na bukatar kudin fito.

Karin bayani