Za a gudanar da taro a kan Girka

Za a yi taro game da tattalin arzikin Girka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tutar kasar Girka

Ministocin harkokin kudi na kasashen da ke amfani da kudin euro za su yi wani taro ranar Litinin a Brussels don yanke shawara a kan baiwa kasar Girka wani sabon tallafin kudi.

A karkashin shirin dai, za a baiwa kasar ta Girka rancen kudi fiye da dala biliyan dari da saba'in, sannan kuma a yafe mata wani bangare na bashin da ake bin ta.

Sai dai takaddama a kan ka'idojin da aka shimfida ta hana cimma yarjejeniya; har yanzu dai bakin ministocin bai zo daya ba a kan yadda za a matsawa kasar ta Girka lamba ta aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu.

A halin da ake ciki kuma an ci gaba da zanga-zangar adawa da sauye-sauye na baya-bayan nan wadanda za su jawo rage albashi da kudin fansho a kasar.

Ana dari-dari game da Girka

Duk da yake dai kasashen da ke amfani da euro na dari-dari game da matakan da Girka ke dauka na tsuke bakin aljihunta, da alama ba su da wani zabi da ya wuce su kara mata rance domin kada ta tsiyace.

Ana sa ran su ma kamfanonin da ke bayar da bashi za su yafe wa Girka kashi saba'in cikin dari na bashin da suke bin ta duk dai domin tattalin arzikinta ya bunkasa.

Sai dai fargabar da ake yi ita ce, duk da daukar wadannan matakai, watakila Girka ta gaza fita daga mummunan halin tabarbarewar tattalin arzikin da ta tsinci kanta a ciki.

Karin bayani