Kasashen yammacin Afrika da Amurka suna atisaye a Gabar Ruwan Guinea

Jiragen yaki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jiragen yaki

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta fara gudanar da wani atisayen hadin gwiwa na kwanaki hudu tare da wasu kasashe goma sha uku da ke makwabtaka da tekun Atlantika, a Calabar da ke kudancin kasar.

Rahotanni na dai, nuna cewa atisayen, wanda kasar Amurka, da wasu kasashen Turai ke halarta, ana gudanar da shi ne don kara inganta harkokin tsaro a kasashen da ke makwabtaka da tekun Atlantika – yankin da ake kira Gabar Guinea ko kuma Gulf Of Guinea.

Ana dai yin wannan atisaye ne bayan kungiyar kula da sufurin jiragen ruwa ta kasa da kasa ke yi wa 'ya 'yanta kashedin akan amfani da tekun da ke kusa da Najeriya saboda karuwar ayukan 'yan fashin jiragen ruwa.

Bayan fashin, yankin yana kuma fama da wasu matsalolin da suka shafi ta’addanci.

Karin bayani