Yau ake zaben shugaban kasa a Yemen

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan kasar Yemen dauke da hoton mataimakin shugaban kasar, Abd Rabbu Mansour Hadi.

Al'ummar Yemen sun fara kada kuri'a da nufin zaben sabon shugaban kasar da zai maye gurbin Ali Abdullah Saleh wanda ya amince ya sauka daga karagar mulki bayan an kwashe watanni ana zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa.

A karkashin wata yarjejeniya da kungiyar hadin kan kasashen yankin Gulf ta shiga tsakani aka cimma, mataimakin shugaban kasar, Abd Rabbu Mansour Hadi, ne kadai dan takara a zaben.

A watan da ya gabata, majalisar dokokin kasar ta Yemen ta amince da wata doka wadda ta baiwa Mista Saleh kariya daga tuhuma, daga nan kuma ya nufi Amurka don a duba lafiyarsa.

'Yan kasar dai sun yi adawa sosai da kariyar da majalisar dokokin ta baiwa Mista Saleh suna masu cewa ya kamata a hukunta saboda laifukan da ya aikata wadanda suka hada da bayar da umarnin kisan jama'a.

Karin bayani