Najeriya za ta iya hako gangar mai miliyan hudu a kullum- Shell

Alamar Kamfanin hakar mai na Shell Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu satar mai ta barauniyar hanya a Najeriya sun taimaka wajen rage yawan danyen man da Kasar ke fitarwa

Najeriya za ta iya hako danyen mai ganga miliyan hudu a kullum, in ba don ayyukan masu satar man ta barauniyar hanya ba.

Sakamakon haka ne Kasar ke hako ganga miliyan biyu da doriya kawai a kowacce rana.

Wani babban jami'in kamfanin mai na Royal Dutch Shell Ian Craig, shine ya bayyana hakan a bukin baje-kolin kamfanonin dake da ruwa-da-tsaki a harkar man fetur a Najeriya.

A cewar babban jami'in, duk da cewar an samu raguwar ayyukan masu tayar da kayar baya a yankin Neja Delta, har yanzu ana samun karuwar barayin danyen mai a yankin.