An yi Allah wadai da kisan 'yan jarida a Syria

Marie Colvin da Remi Ochlik Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Anyi Allah wadai da kisan 'yan jarida a Syria

Shugabannin kasashen yamma sun yi Allah wadai da kisan da aka yiwa daya daga cikin 'yan jaridar duniya da suka shahara wajen aikewa da rahotanni daga fagen yaki, Marie Colvin da kuma wani dan kasar Faransa Remi Ochlik a birnin Homs dake Syria.

Sun rasa rayukansu ne a lokacin da dakarun Syria suka yiwa wani wuri da suke aikewa da rahotanni a Unguwar Baba Amr luguden wuta.

Amurka tayi Allah wadai da abinda ta kira musgunawa wadda abun kunya ce ga gwamnatin shugaba Assad.

Masu fafutika sun ce an kashe 'yan jaridar ne a lokacin da dakarun Syria suka yiwa wani gida da suke aikewa da rahotanni a Unguwar Baba Amr luguden wuta.

Kashe-kashen na baya-bayan nan a Syria sun zo ne jim kadan bayan da Amurka ta yi gargadin cewar za ta iya kara daukar matakai a kan Syria idan Shugaba Assad bai kawo karshen tashin hankalin ba.

A ranar Talata ne Ms Colvin ta bayyana halin da ake ciki a birnin Homs a matsayin abin damuwa matuka, tana mai cewar lugudan wutar da dakarun gwamnatin keyi na nuni da rashin tausayi da mutanta fararen hula.

An kuma hallaka wani mai fafitika a kasar ta Syria, Rami al Sayed wanda ke samar da wasu faya-fayen bidiyon abinda ke faruwa a birnin na Homs.

Ministan harkokin wajen Faransa Alain Juppe ya ce zai gudanar da bincike kan yadda aka hallaka Remi Ochlik.

Matsin lamba kan Syria

"Ina mai matukar nuna jimami da ta'aziyya ta ga iyalan dan jaridar kasar Faransar, zan yi kokarin in gano takamaiman musababin wannan kisa.Wannan ya dada nuni da yadda al'amura suka kara tabarbarewa a kasar Syria".

Wata mamba a kwamitin Majalisar gwamnatin rikon kwaryar kasar Syria, Basma Kodami ta ce ta yi amannar cewar masu goyon bayan gwamnati ne suka hallaka 'yan jaridar.

"A Yanzu babu wasu shaidu a kasa kamar 'yan jaridun kasashen waje, kuma jama'a da dama na son ganin cewar kafafen yada labarai sun bayyana zahirin abubuwan dake faruwa, saboda haka ban ga dalilin da zai sa a kashe 'yan jaridar ba.

Ni nayi amannar cewar mutanen dake da alaka da gwamnati ne suka aikata wannan domin hana 'yan jaridu gudanar da aikin su a birnin Homs, ta tabbata cewar da ganagan shugaban Syria Bashar Al Assad ke kokarin mayar da birnin Homs ya zama wani mahawayi ga 'yan jarida".

Wannan lamari dai na faruwa ne a daidai lokacin da Amurka ke gargadin tare da yin barazana ga mahukuntan kasar ta Syria na daukar tsauraran matakai idan basu kawo karshen hare-haren da dakarun gwamnatin ke kaiwa a birnin na Homs ba.

Karin bayani