Yau ake soma babban taro kan Somalia a birnin London

Kasar Somalia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron Kasashen duniya akan rikicin Somalia

Yau ne za a fara wani taro na Kasashen duniya a London a game da makomar Kasar Somalia.

Wannan wani yunkuri ne da Firayim Ministan Burtaniya David Cameron ke jagoranta don nemo sabbin hanyoyin da za a kawo karshen yamutsi da yunwa da yakin basasar da aka shafe sama da shekaru ashirin ana gwabzawa a Kasar.

Wakilai na gwamnatin rikon-kwarya da Kungiyoyi daban-daban ne za su halarci taron, amma banda Kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Al Shabab wadda ke da ikon mafi rinjayen tsakiya da kuma kudancin Kasar ta Somalia.

A waje daya kuma dakarun Habasha da taimakon sojan gwamnatin rikon kwaryar Somalia sun kwace ikon mulki da birnin Baidoa dake tsakiyar Kasar a hannun mayaka na Kungiyar Kishin Islama ta AlShabab.

Sun kwaci birnin ne salun-alun ba tare da wani fada ba lokacin da mayakan na Al Shabab suka arce daga yankin suna cewar maimakon fadan, za su koma yakin sari-ka-noke

To amma masu aiko da rahotanni sun ce hakan wani babban koma-baya ne ga Kungiyar ta AlShabab.

Karin bayani