An nada Kofi Anan wakili na musamman ga Syria

Kofi Annan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kofi Annan zai yi kokarin kawo karshen zubar da jini a Syria

An nada tsohon babban Sakataren Majalisar dinkin duniya Kofi Annan a matsayin wakilin hadin-gwiwa na musamman na Majalisar dinkin duniyar da kuma Kungiyar Kasashen Larabawa ga Kasar Syria.

Mr. Kofi Annan zai yi aiki ne karkashin babban sakataren majalisar dinkin duniya Banki Moon da kuma Sakataren Kungiyar Kasashen larabawa.

Wata sanarwar hadin gwiwa data fito daga bangarorin biyu, tace Mr. Annan zai yi kokarin kawo karshen tashe- tashe hankulan dake aukuwa a Kasar ta Syria da kuma kawo karshen yadda ake keta hakkin dan- adam.

Nadin wakili na musamman ga Syrian na daya daga cikin hanyoyin da Kasashen yammacin duniya da kuma Kasashen larabawa suka yanke shawarar dauka akan syrian, bayan da Kasashen Rasha da China suka hau kujerar naki game da wani kuduri na kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya da ya goyi bayan shirin Kungiyar Kasahen larabawan.

Mr. Annan ya yi aiki a matsayin babban sakataren majalisar dinkin duniya daga shekara ta 1997 zuwa shekara ta 2006.

Ya kuma karbi kyautar Nobel ta zaman lafiya saboda aikin da ya yi na yaki da cutar AIDS.

Karin bayani