An kirkiro da sabon maganin yaki da cutar Malariya a Najeriya

Zazzabin cizon sauro Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Masana kimiyya a Najeriya sun gano maganin zazzabin malariya

A Najeriya, masana kimiyya a jami'ar Jos dake jahar Filato, sun kirkiro da wani sabon maganin cutar zazzabin cizon sauro ko kuma malariya.

Masana kimiyyar dai sun shafe shekaru biyu su na gudanar da bincike tare da hadin-gwiwar bankin duniya.

Masanan dai sun samu nasarar noma wata itaciya wadda ake kira 'Artemissia annua', wadda kafin yanzu ake nomawa a Kasashen China da indiya da wasu Kasashe na gabashin Afirka.

Cutar Malariya dai ta dade tana addabar mutane a nahiyar Afirka musamman ma yankunan kudu da hamadar Sahara.

Farfesa Hayward Mafuyai, shine mataimakin Shugaban jami'ar jos, kuma daya daga cikin masana kimiyyar da suka yi binciken.