'BBC na tafiya da zamani'

  • Daga Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik)
  • Masanin harkokin internet
BBC na tafiya da zamani

Asalin hoton, other

Bayanan hoto,

Hanyoyin sadarwa na zamani na taka rawa wajen yada labarai da sada zumunta

A tabbace yake cewa hukumar tashar BBC na tafiya ne da zamani wajen tsarawa, da ingantawa, da kuma watsa shirye-shirye.

Daga tsarin sauti ko tashar talabijin mai amfani da tsarin Analogue da a shekarun baya ake amfani da su, a yanzu tsarin watsa shirye-shirye sun samu karin tagomashi.

Duk wata fasahar sadarwa da ka sani a duniya a yanzu kana iya amfani da ita wajen sauraro ko kallon shirye-shiryen BBC.

Wannan ya faru ne saboda amfani da hanyoyin sadarwa na zamani masu inganci da tashar ke yi wajen watsa shirye-shiryen, da saukake hanyoyin samunsu musamman ga jama'ar da ke kasashe masu tasowa.

Daga cikin ingantattun tsarin da BBC ta kula da su akwai bangaren sauti da kyautata shi.

Facebook da Twitter

Sai fadada harsuna, da kuma karantar da harshe cikin dabara, ta hanyar amfani da kalmomin da suka dace da zamani, wajen watsa shirye-shirye.

Da amfani da tauraron dan adam musamman na Nilesat a nan nahiyar Afirka. Sai tsarin Video Phone, don ganawa da masu aiko rahotanni ta kai tsaye a sako-sako na duniya.

A daya bangaren kuma tashar ta kyautata tsarin kusantar da labarai ta hanyoyi da dama. Misali, ta inganta babban shafinta da ke Intanet, inda za ka je ka samu shirye-shiryen da aka gabatar a baya; na rediyo ne, ko na talabijin. Sannan ga hotuna rau-rau masu kayatarwa.

Sun kuma bude shafi a dandalin Facebook da Tweeter inda duk masu sauraro ke iya zuwa don fadin albarkacin bakinsu, bayan labarai da ake zubawa da dumi-duminsu.

Sai kuma hanyar da tafi kowacce gamewa, watau hanyar amfani da wayar salula don karban sakonnin tes daga masu sauraro.

Amfani da kowacce fasaha

Hakika wannan yana tasiri sosai a tsakanin masu sauraro, domin da dama cikin sakonnin da BBC ke karba daga masu sauraro a kasashenmu (Najeriya, da Nijar, da Ghana, da sauransu), duk ta hanyar sakonnin tes ne. Wannan ya dada taimakawa wajen kusantar da masu sauraro matuka.

A takaice dai ma iya cewa, duk wata kafa da ake iya samun labarai ko watsa su a duniya, ko wata fasaha da ake amfani da ita wajen watsa shirye-shirye a wannan zamani, tashar BBC na amfani da su wajen samarwa da kuma kusantar da su ga jama'a a yau.

Daga tashar rediyo ta Short Wave (SW), da tsarin watsa shirye-shiryen rediyo ta Intanet (Internet Radio), da fasahar Podcast, da tashar FM, da tsarin watsa shirye-shiryen rediyo da talabijin ta tauraron dan adam (Satellite TV & Radio), har zuwa tsarin samar da shirye-shiryen rediyo ta ingantacciyar sauti (HD Radio), duk BBC ta bi wajen ingantawa da kusantar da shirye-shiryenta ga masu bukata.

A yau kana iya sauraron shirye-shiryensu a rediyo, ko ka kalla a talabijin, ko a wayar salula ta gama-gari, ko nau'in iPhone, ko iPad, a mitoci na 16, da 19, da 22, da 25, da 31, da 41, da kuma 49.

A kullum nayi la'akari da wadannan ingantattun hanyoyin sadarwa da BBC ke samarwa, da tsarin saukake samun labarai da dumi-duminsu, da kuma kokarin tabbatar da gaskiya ta hanyar bayar da kyakkyawar karantarwa ga ma'aikata, sai in tuna shekaru 22 da suka gabata, lokacin da na fara sauraren tashar ta hanyar 'yar karamar rediyo, sannan ina sakandare.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana iya samun labaran BBC a wayoyin salula ko kwamfiyutar hannu a duk inda kake

Na lazimci shirye-shiryen BBC musamman na Turanci, saboda karin kwarewa da nake samu wajen furuta wasu kalmomin turancin. Na saba da galibin 'yan sashen turanci irinsu Julian Marshall, da Mary Small, da Debra Mackenzie, da Sandy Walsh, da Helen Thomas da ke sashen Tarihi, da Zainab Badawi, da kuma gwarzon matasa, watau Steve Wright, wanda ba na kuskure shirinsa mai suna Wright Round the World a duk karshen mako.

Na shaku da shirye-shiryen sashen turanci sosai, irinsu Newshour, da One Planet, da Outlook, da Science in Action, sai kuma shirin koyon harshen Turanci mai suna The Learning Zone.

A hakikanin gaskiya, sanadiyyar wannan shiri na karshe ne na fara mu'amala da fasahar Intanet, ta hanyar Imel.

A bangaren sashen Hausa ma na amfana matuka, domin har littafi na ajiye inda nake rubuta muhimman labarun da nake saurare, tunda babu fasahar Intanet a kasar, ba ni da talabijin balle in sa tauraron adam; daga 'yar karamar rediyo sai littafi na.

Da zarar Sale Halliru, ko Suleiman Ibrahim Katsina, ko Jameela Tangaza, ko Mansur Liman ko Mannir Dan Ali, ko wani daga cikin 'yan sashen Hausa ya fara labaru, sai in fara rubutawa nan take. Idan aka gama shirye-shiryen, sai in dauko littafi na ina bita.

Na shaku matuka da shirin Amsoshin Tambayoyinku, da shirin Taba-kidi Taba-karatu. Duk ta haka nake taskance su.

Amma a yau cikin yardar Allah, kuma a daidai lokacin da tashar ke shirin bikin murnar cika shekaru 80 da fara watsa shirye-shiryenta, ina iya sauraronsu ta wayar salula, ko ta kwamfuta, ko in kunna talabijin don kallon shirye-shiryensu, da zarar lokacin sashen Hausa yayi kuma, sai in haura zuwa tauraron dan adam don kamo su; abin da a shekarun baya ban taba mafarkinsa ba.

Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik)

Mai nazari ne kan harkokin sadarwa na zamani a Najeriya