Hillary Clinton ta soki Kasashen Rasha da China

Hillary Clinton
Image caption Hillary Clinton ta bayyana cewar Kasashen Rasha da China sun nuna karanta

Sakatariyar kula da harkokin Kasashen wajen Amurka Hillary Clinton, ta yi kakkausar suuka ga Kasashen Rasha da China.

Hillary Clinton ta ce karanta ce a gare su, su bijire wa matakin da kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniya ya yi niyyar dauka a kan gwamnatin Syria a daidai lokacin da sojojin Kasar ke hallaka mutane.

Mrs. Clinton ta kuma yi nunin cewa Rasha tana da kamasho, saboda ita ce ke baiwa Kasar ta Syria makamai.

Karin bayani