Ana zaben gwamman jahar Cross River

Zabe a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zabe a Najeriya

A Nijeriyar a yau ne ake gudanar da zaben gwamna a jihar Cross River dake kudu maso kudancin kasar.

Zaben dai ya biyo bayan hukuncin kotun kolin kasar ne wanda yace wa'adin gwamna mai ci, Sanata Liyel Imoke ya kare tun bara.

An dai tura jami'an tsaro dadama zuwa sassa daban daban na jahar domin tabbatar da an yi zaben lami lafiya.

Jama'a da dama ne dai basu fito zabenba, wanda sukai zargin tuni aka riga aka san kowaye zai yi nasara.

Nan zuwa gobe lahadi ne ake saran bayyana sakamakon zaben gwammnan na jahar Cross River.

Karin bayani